18 Janairu 2015 - 11:27
TARON  KADDAMAR DA ASUSUN GININ MATATTARAR IMAM RIDHA(AS) A GARIN KADUNA NIGERIA

TARON KADDAMAR DA ASUSUN GININ MATATTARAR IMAM RIDHA(AS) A GARIN KADUNA NIGERIA

A jiya ne 17th ga Janairu 2015 ne Mu’assasar Thaqafar Thaqalayn Kaduna karkashin jagorancin  Shaikh Hamzah Muhammad Lawal ta kaddamar da asusun fara ginin Matattarar Imam Ridha wato Mujamma’ul Imamir Ridha Kaduna Nigeria.

An fara taron ne da budewa da addu’a daga bakin Malam Haruna Dinya,sai kuma karatun Alkur’ani daga bakin dan uwa  Alaramma Malam Tahir Abdullahi Kano,sai kuma Malam Muhammad Uba ya gabatar da babban sakataren Mu’assasar da Manyan bakin taron.

Bayan haka ne Malam Rufa’i Sule Bichi,shugaban taron ya gabatar da  Shaikh Hamzah Lawal domin gabatar da jawabi game ita Mujamma’ul Imamir Ridha Kaduna Nigeria.

 Shaikh Hamzah yayi jawabi na tsawon mintina talatin da takwas da farko sannan a dawo wa ta biyu yayi kimanin mintuna goma sha tara,Daga cikin abubuwan da Shaik ya fadi, yace mun zabi watan haihuwan Manzon Allah(saw) don kaddamar da ita gidauniyar domin samun tabarruki da Rahmar Manzon Allah ta gamagari,sannan ya fadi dalilin da yasa aka zaba ma ita Matattarar sunan Imam Ridha,inda yake cewa shi Imam Ridha ya kasance daya daga cikin jikokin Manzon Allah wanda shi kofa ne na biyan bukatu da waraka daga cututtuka a lokacin da yake a raye da bayan wafatinsa har malam ya kara da bada hujjoji daga Manya manyan malaman Ahlus-sunna(wato A’alam a sunnah) wadanda suka yi I’itirafi da kasantuwar Imam Ridha kofa na biyan bukatu da waraka daga cututtuka.

A cikin jawabin na  Shaikh Hamza ya fadi abubuwan da ake so ayi a wannan fili wanda aka mallaka wanda ya kai hecter 2.1 a garin Kaduna Nigeria.Yace za ayi Makarantan gaba da primary ta kwana guda biyu,daya na mata daya na maza,da kuma babban masallaci wanda zai dauki mutane masu yawa,da cibiyar Al-thaqalayn Cultural Foundation Kaduna Nigeria, da dakin taro wanda za a iya komai a cikinsa da sauran abubuwa.

Ya cigaba da cewa mutane su taimaka saboda ba za ayi makarantar domin neman riba bane,babban hadafin ginin shine tarbiyyantar da al-umma domin kowane shekara a a kasafin kasa ana ware  biliyoyin kudi ga mawaka da yan fina finai domin bata tarbiyyan yara.

Shaikh Hamza yayi nuni akan hanyoyi masu yawa na taimawa kamar abinda ake kira da Waqafi,Wasiyya,Sadaka,Kyauta daZakka a shari’ar musuluncin domin taimakon wannan Mashru’i na rayuwa.Sannan yace Alhamdulillah mutane sun koya yanda ake mu’amala da banki,sannan sun nemi banki ya basu POS kuma za a basu kuma da an basu zasu aikawa da mutane domin saukakewa  ga wajajen da bankuna.

Shaikh ya yaba da kokarin jama’a na sadaukarwa ta kowacce hanya sannan kuma yayi fatan alkhairi ga kowa da kowa da addu’a,sannan ya kara da cewa barci bai ganmu ba domin yanzu za a fara aikin saboda haka mutane su shirya.

Bayan Shaikh ya kammala jawabinsa sai aka bude gidauniyar da kaddamarwan wata Dattijuwa mai albarka na naira 200.Daga nan ne mutane suka fara fitowa suna kaddamarwa,masu daruruwa na badawa masu dubbanni na badawa masu miliyoyi na bada,wasu kuma filaye suke badawa wasu kuma kayan noma suke badawa wasu kuma littafai da sauransu da sauransu.Wani bawan Allah wanda bai so a ambaci sunansa ya kaddamar  akan zai yi aikin fiye da miliyan 40 a filin ta hanyar yin Katange filin dukkansa  da fitar da hanyoyi da sauransu da sauransu.

Bayan kammala Kaddamarwan ne aka kira Shaikh Tahir domin jawabin godiya ga mahalarta taron,bayan nan kuma aka rarraba abinci da abubuwan sha ga mahalarta taron,daga nan kuma sai Malam Rufa’i  ya fadawa jama’a jimillar abinda aka tara cewa an samu zunzurutun kudi naira na gugan naira har miliyan 49 da yan kai banda wancan bawan Allah da zai yi aikin fiye da miliyan 40 a filin.Sai daga karshe aka kira Shaikh Ibrahim Mu’azzin domin gabatar da rufe taron da addu’a.ABNA

Taron kaduna

Taron kaduna

Taron kaduna

Taron kaduna

Taron kaduna

Taron kaduna